OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Shugaba Buhari Ya Taya Tsohon Shugaban Kasa Babangida Murnan cika Shekaru 81 a Duniya

Photo Source:The Will

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mika sakon gaisuwa ga tsohon shugaban kasar Najeriya a mulkin soja, Ibrahim Badamasi Babangida domin murnar cikar sa shekaru 81 a duniya a gobe 17 ga watan Agusta na 2022.

Shugaban ya aika da sakon murnan ne cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Femi Adesina ya fitar a ranar Talata.

Buhari ya bayyana cewa Babangida ya taka rawar gani sosai wajen ci gaban kasan nan. 

A cewar sanarwar, “Shugaba Buhari yana taya ‘yan uwa da abokan arziki da kuma abokan huldan tsohon shugaban domin murnar karin shekara guda, da yardar Allah da kuma rahamar sa.

“Shugaban ya lura da irin rawar da tsohon shugaban kasa na mulkin soja ya taka a tarihi wajen samar da ci gaban siyasa da tattalin arzikin kasar nan, da shawarwarin sa ga shugabannin siyasa masu zuwa.

"Shugaba Buhari yayi addu'ar Allah ya karawa shugaban nisan kwana, lafiya da karfin jiki."

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci