OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Shugaba Buhari Ya Mika Sakon Ta'aziyya Ga Iyalan Sarauniyar Ingila

Shugaba Buhari Ya Mika Sakon Ta'aziyya Ga Iyalan Sarauniyar

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana alhinin shi bisa rasuwar Sarauniyar Ingila Elizabeth ta biyu, inda ya ce ya samu labarin rasuwar da bakin ciki matuka.

Sarauniyar da ta fi dadewa a kan karagar mulki a tarihin kasar Birtaniya ta rasu a ranar Alhamis din da ta gabata.

Kunshe a cikin sakon ta’aziyyar da ya aike ta hannun mai magana da yawunsa Garba Shehu a Abuja, Buhari ya kira shekarun da ta yi shugabanci a matsayin abin al’ajabi.

 "Ni da iyalina, da 'yan Najeriya sama da miliyan 200 mun samu labari mai muni da bakin ciki game da rasuwar Sarauniyar da kuma karshen mulkinta na musamman na shekaru 70. Marigayi Elizabeth ita kadai ce Sarauniyar Burtaniya wanda kashi 90 cikin 100 na al'ummarmu suka sani.

Tunaninmu da ta'aziyyarmu na tare da dangin ta da jama'ar Burtaniya da sauran kasashen Commonwealth yayin da muke taya duniya baka daya jimamin rashin ta"

 Shugaban kasan ya Kara da cewar "Labarin Najeriya na zamani ba zai taba cika ba sai da wani babi kan Sarauniya Elizabeth ll, wadda ta kasance ta musamman a duniya kuma fitacciyar shugaba da ta sadaukar da rayuwarta wajen kyautata rayuwar Al'ummar ta da Al'ummar kasashen commonwealth baki daya" in ji shi.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci