OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 4 Kwanaki da suka gabata

Saudiyya Ta Musanta Dakatar Da Umrah A Bana

Saudiyya Ta Musanta Dakatar Da Umrah A Bana

Mahajjata

Hukumomi a Saudiyya sun ce labarin dakatar da Umara saboda yaduwar cutar korona ba gaskiya ba ne.

Wata majiya a ma’aikatar Hajji da Umrah ta kasar ta shaida wa Haramain Sharifain cewa ba ta da niyyar dakatar da aikin umarar.

A baya-bayan nan ne dai fadar shugaban Saudiyya dake mai kula da harkokin masallatai biyu masu alfarma ta sake amince da dawo ta’zaara tsakanin mutane a Masallatan Harami guda biyu bayan da aka samu karuwar masu dauke da cutar COVID-19, sannan ta yi kira ga mahajjatan da su bi matakan kariya da hukumomin da suka dace suka dauka. .

Ko a ranar Alhamis, Limamin Masallacin Harami Sheikh Yasir Al Dossary daf da fara gabatar da sallah sai da ya yi kira  sanya takunkumi da kuma bayar da tazara tsakanin masallatan, wanda a cewar sa haka zai tabbatar da tsaron ku da lafiyar sauran.

Saudiyya ta ba da sanarwar mutuwar mutane biyu daga cutar Korona daga cikin mutum 5,499 da suka kamy da ita a ranar Alhamis.

Cikin wannan adadi, mutum 1,565  ne aka samu a Riyadh, sai mutum 877 a Jeddah, a Makkah kuma an samu mutum 474 , 239 a Madina, 198 a Dammam, 137 a Taif, 110 a Qatif, 103 a Al-Khobar, 102 a Hofuf, 100 a Khulais. Wasu garuruwa da yawa sun sami adadin wadanda suka kamu da cutar kasa da dari.

Adadin wadanda suka warke daga cutar ya karu zuwa 555,035 bayan wasu karin marasa lafiya 2,978 sun murmure daga ita.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci