OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 2 Shekaru da suka shude

Ba Bakon Lamari Ne Samun Hadiman Shugaban Kasa Da Cutar Korona Ba — Fadar Shugaban Kasa

Ba Bakon Lamari Ne Samun Hadiman Shugaban Kasa Da Cutar Koro

Femi Adeshina

Fadar Shugaban kasa ba sabon abu bane samun masu dauke da kwayar cutar korona cikin hadiman  Shugaba Buhari, kamar yadda yanzu haka suka killance kawunan su a gidajen su.

 

Mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Femi Adesina ne ya sanar da haka ranar Lahadin ta cikin shirin a gidan talabijin na Channels, ya kara da cewa haka wani tabbaci ne na cewa mataimakan shugaban kasa mutane kamar kowa.

 

Idan za’a iya tunawa a ranar Asabar haridar Premium times ta rawaito cewa wasu hadiman shugaban kasa na dauke da cutar korona, ciki har da ministan yada labarai da al’adu, Alhaji Lai Mohammed.

Sai dai ministan ya musanta labarin, inda ya nemi jaridar ta janye labarin sannan ta nemi afuwar sa bisa zargin wallafa labara maras tushe.

 

Da yake Karin bayani, babban mai taimaka wa shugaban kasa kan harkokin yada labarai Malam Garba Shehu, ya ce ba shi da tabbacin sauran takwarorin sa da aka ce suna dauke da cutar, amma shi ya kamu da ita amma da sauki.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci