OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 2 Shekaru da suka shude

Rundunar ‘Yan Sanda Ta Kama Wata Mata A Hanyar Kai Makamai Ga ‘Yan Bindiga A Jihar Zamfara

Rundunar ‘Yan Sanda Ta Kama Wata Mata A Hanyar Kai  Makama

Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ta cafke wata mata mai shekaru 30 a hanyar kaiwa ‘yan bindihga makamai da alburusai jihar Zamfara.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Ayuba Elkana ne ya bayyana hakan a ranar Juma’a yayin holin matar a Gusau, inda ya ce an kama matar mai suna Fatima Lawali a ranar Alhamis, 25 ga watan Oktoba da misalin karfe 9:30 na dare.

Kwamishinan ya ce an kama matar da ake zargi da alburusai da bindiga kirar AK-47 daga kauyen Dabagi a jihar Sokoto, zuwa ga wani shugaban ‘yan bindiga, Ado Alero wanada da ya dade yana kai hare-hare yankunan Zamfara da makotan jihar.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci