OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Rashin Tsaro: 'Yan Bindiga Sun Sace Mutum Biyu A Jihar Kwara

Rashin Tsaro: 'Yan Bindiga Sun Sace Mutum Biyu A Jihar Kwara

Biyo bayan farmakin da wasu ‘yan bindiga suka kai a unguwar Aseyori da ke yankin Alagbado a jihar Kwara, an sace yara biyu.

A cewar rahoto, ‘yan bindigan da yawan su ya haura 6, sun kai farmaki gidan wani dillalin jari bola mai suna Lukman Aliyu da misalin karfe 12 na dare.

Maharan da suka yi ta harbe-harbe a lokacin farmakin sun yi awon gaba da ‘ya’yan Aliyu guda biyu masu suna Quadir mai shekaru 15 da Muideen mai shekaru 12.

Da yake tabbatar wa Daily Trust faruwar lamarin, mahaifin yaran, Aliyu ya ce: “Ban ma san yadda na rayu ba saboda sun yi ruwan harsashi akan gidan.

“Na boye matata da ’ya’yana biyar a daya daga cikin dakunan na gudu wani waje amma sun yi balle katako da gatari suka lalata kofar ta kasa don samun shiga.

“Sun dauki biyu daga cikin yaran suka bugi matata a kirji sosai. 

“Sun tafi da wayoyi hudu kuma sun tuntube mu suna neman kudin fansa naira miliyan 20.

"Wannan shi ne karo na uku da ake yin garkuwa da mutane cikin makonni a yankin kuma mazauna yankin sun yi watsi da dukiyoyin su saboda fargabar yin garkuwa da su."

A halin yanzu dai rundunar ‘yan sandan jihar Kwara ba ta fitar da wata sanarwa ba.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci