OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

NBC: Gwamnatin Zamfara Ta Cika Bashin Naira Miliyan 25

NBC: Gwamnatin Zamfara Ta Cika Bashin Naira Miliyan 25

Governor Bello Matawalle of Zamfara State

Gwamnatin jihar Zamfara ta biya Naira miliyan 25 da hukumar yada labarai ta kasa (NBC) ke bin ta daga shekarar 2017.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kwamishinan yada labarai na jihar Hon. Ibrahim Magaji Dosara ya fitar. 

A cewar sa, gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle ya amince da gaggauta biyan basussukan a makon da ta gabata. 

Kwamishinan ya kara da cewa tuni aka biya hukumar kudaden a ranar Juma’a.

A cewar sa: “Kudaden da aka riga aka biya a asusun hukumar a ranar Juma’an makon da ta gabata, wani bangare ne na alkawuran da gwamnati ta yi na ci gaba da kyautata alakar aiki da hukumar da sauran kafafen yada labarai domin tabbatar da an sanar da mutane cikakkun shirye-shirye da manufofin gwamnati na ci gaban Jihar”.

Yayin da yake taya al’ummar Zamfara murnar samun gwamna mai sanin yakamata, Dosara ya kara da cewa gwamnatin jihar ta biya Naira miliyan 5 a shekarar da ta gabata daga cikin Naira miliyan 37 da hukumar NBC ke bin ta. 

Ya kuma yi kira ga jama’a da su ci gaba da yi wa gwamnatin jihar addu’a domin samun nasara.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci