OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Mutum Biyar Sun Mutu Yayin Da Suke Tserewa Daga Hannun 'Yan Bindiga A Abuja

Mutum Biyar Sun Mutu Yayin Da Suke Tserewa  Daga Hannun 'Yan

Wasu mutane biyar da suka hada da maza magidanta hudu da matar aure daya sun nutse a ruwa a kokarinsu na tserewa daga hannun ‘yan bindiga da suka yi garkuwa da su a kauyen Chakumi da ke unguwar Gurdi a karamar hukumar Abaji a Abuja.

Shugaban kauyen Chakumi, Mohammed Magaji, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 11 na safiyar Laraba.

Ya ce wadanda lamarin ya rutsa da su, ciki har da wata mata mai matsakaicin shekaru suna aiki a gona, sai suka ga ‘yan bindigar.

Sarkin ya ce sun garzaya ne suka hau kwalekwale domin tserewa zuwa kauyen Daku da ke makwabtaka da shi, amma a kokarin da suke na tsallakawa kogin Gurara sai kwale-kwalen ya kife.

“Kuma ko da nake magana da ku a halin yanzu, gawarwakin wadanda abin ya shafa har yanzu ba a gano su ba, yayin da masunta daga Daku da kauyenmu ke ci gaba da neman gawarwakin,” inji shi.

Magaji, wanda ya koka kan ayyukan ‘yan bindiga a yankin, ya ce manoma ba za su iya zuwa gonakinsu ba saboda fargabar ‘yan bindiga su yi garkuwa da su.

Shi ma mataimakin shugaban karamar hukumar Abaji, Ibrahim Abubakar, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya bayyana cewa daya daga cikin ‘yan uwansa na cikin wadanda suka nutse.

"Hakika, daya daga cikin 'yan uwana na cikin wadanda suka nutse kuma har yanzu ba a gano gawarwakinsu ba har zuwa yanzu da nake magana da ku," in ji shi.

Kakakin rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja, DSP Adeh Josephine, bata ce komai kan lamarin ba duk da saƙonnin da aka aike mata.

 

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci