OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 2 Shekaru da suka shude

Mutane Tara Sun Rasu A Hare-Hare Mabambamta Kan Kauyuka Uku A Jihar Sokoto

Mutane Tara Sun Rasu A Hare-Hare Mabambamta Kan Kauyuka Uku

Rundunar ‘yan sandan jihar Sokoto ta tabbatar da sace mutane tara a hare-hare mabambamta da ‘yan bindiga suka kai kauyuka uku dake karamar hukumar Sabon Birni.

 

Da yake zantawa da manema labarai kan hare-haren a ranar Alhamis, jami’in hulda da jama’a na rundunar, ASP Abubakar Sanusi ya ce ‘yan bindigar sun kai hare-haren da suka yi sanadiyyar rasa rayukan ne a ranakun 15, 16, da kuma 17 na watan Nuwamban shekara ta 2021.

 

ASP Sanusi ya ce an kai harin farko Garin Zago dake karamar hukumar Sabon Birni, inda aka kashe mutane uku, aka kuma sace wasu mutum uku.

 

An kuma kai hari na biyu kan wani abin hawa a kauyen Gaji, amma ba’a raunata ko kashe ko sace kowa a wannan harin ba.

 

Jami’in ya cigaba da bayyana cewa an kai hari na kauyen Sangirawa, inda aka kashe mutane shida, aka ‘yan bindigar suka kuma raunata wasu da dama.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci