OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Jiragen saman NAF sun yi nasarar kashe dan ta'adda Ali Dogo, da wasu mutanen sa a Kaduna

Jiragen saman NAF sun yi nasarar kashe dan ta'adda Ali Dogo,

Rahotanni daga jaridar PRNigeria ta ruwaito cewa, an kashe fitaccen shugaban ‘yan bindigan nan Ali Dogo tare da mutanen sa su 30 a wani harin da sojojin saman Najeriya suka kai musu ta sama.

An gano cewa, Dogo, wanda aka fi sani da Yellow, tare da ‘yan kungiyar sa, an samu lagon su ne sakamakon harin da rundunar sojin sama ta Operation WHIRL Punch ta kai a karshen mako.

Kamfanin dillancin labarai na PR ya ruwaito a shafin su na yanar gizo ta majiyar leken asiri cewa fitaccen shugaban ‘yan ta’addan da tawagar sa sun tsere ne daga jihar Neja zuwa gidan wani Alhaji Gwarzo da ke unguwar Yadi a karamar hukumar Giwa domin tsira da rayukansu, biyo bayan harin da jiragen saman NAF suka kai musu a jihar Niger a kwanakin baya.

Majiyar ta ce, "Abin da ya faru shine Yellow da mutanensa, suna tsaka da gudanar da taro,ne jirgin na NAF ya kai musu hari a gidan Alhaji Gwarzo, wanda aka yi nasarar tarwatsa duka wadanda suke cikin gidan hadda shi Yellow."

Rahoton sun bayyana cewa Kakakin Rundunar Sojojin Sama, Air Commodore Edward Gabkwet, ya tabbatar da nasarar da aka samu, inda yace “Rundunar sojin sama bisa umarnin Shugaban Hafsan Sojan Sama, Air Marshal Oladayo Amao, za ta ci gaba da kai hare-hare a kan irin wadannan masu aikata laifuka tare da hadin gwiwar sauran jami’an tsaro.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci