OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Majalisar Dattawa ta tabbatar da Ariwoola a matsayin shugaban Alkalai na Najeriya

Majalisar Dattawa ta tabbatar da Ariwoola a matsayin shugaba

Majalisar Dattawa ta tantance tare da tabbatar da Alkalin Alkalan Najeriya (CJN), Mai Shari’a Olukayode Ariwoola.

Tabbatarwar ya biyo bayan amsa tambayoyin da Sanatoci suka yi masa da misalin karfe 12:45 na rana.

In ba a manta ba shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar 26 ga watan Yuli shekarar 2022 ya aikawa majalisar Dattawa ,wasika akan a tantance tare da tabbatar da Mai Shari’a Olukayade Ariwoola wanda a halin yanzu yake rike da mukamin Alkalin Alkalai na Najeriya.

Wasikar mai dauke da kwanan watan 25 ga watan Yuli, 2022 wanda shugaban majalisar Dattawa Ahmad Lawan ya karanta.

Wasikar ta kasance kamar haka, “Bisa ga sashe na 231 (1) na kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya na shekarar 1999 wanda aka yi wa kwaskwarima na gabatar wa majalisar dattawa Mai shari'a Olukayode Ariwoola a matsayin alkalin alkalan Najeriya.

Nadin Justice Ariwoola a matsayin Alkalin Alkalai da shugaba Buhari yayi ya biyo bayan murabus din da tsohon Alkalin Alkalai Muhammad Tanko yayi a ranar 27 ga watan Yuni, 2022.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci