OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Ma'aikatan Muhalli Sun Yi Barazanar Rufe Maƙabartun Abuja

Ma'aikatan Muhalli a babban birnin tarayya Abuja sun yi barazanar rufe dukkan maƙabartun gwamnatin dake birnin.

Sun bayyana ɗaukar matakin kan ƙin biyan su sabon tsarin albashi da hukumomin babban birnin tarayyar suka yi.

Da yake ƙarin haske kan dalilan matakin, Shugaban gamayyar kungiyoyin Muhallin birnin tarayyar, AUPCTRE, Mukhtar Bala ya ce suna shirye-shiryen rufe dukkan maƙabartun dake babban birnin tarayya matuƙar ba'a biya musu buƙatun su ba.

Ya ce sam ma'aikatan ba sa son yadda hukuma tayi wasarere da lamarin su ba, inda yace matakin da suka ɗauka ya biyo bayan sahalewar uwar ƙungiyar su ta ƙasa.

"Mutane suna tsammanin kwashe shara ne kawai aikin mu, ba su san gawarwakin da ba'a san ƴan uwan su ba ma mune ke da alhakin kula da su", kamar yadda Mista Bala ya shaidawa Daily Trust.

Ya ce aikin su na jefa rayuwar su cikin haɗari ganin yadda suke kula da gawarwakin da suka shafe shekaru ba tare da masu su sun karbe su tare da binne su ba.

Tun da faru dai kungiyar ta garƙame wata maƙabarta a Abujan, inda daga bisani suke buɗe ta bayan mahukunta sun lallashe su.

 

 

 

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci