OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Kasafin Kudin 2023: Delta Ta Ware N111.4bn Don Samar Da Ababen More Rayuwa

Kasafin Kudin 2023: Delta Ta Ware N111.4bn Don Samar Da Abab

Gwamna Ifeanyi Okowa na jihar Delta ya ce gwamnatin jihar ta ware naira biliyan 111.4 ga ma’aikatar ayyuka domin gudanar da ayyukan raya ababen more rayuwa a shekarar 2023.

 Okowa ya bayyana hakan ne a lokacin da ya gabatar da kasafin kudin jihar na shekarar 2023 na Naira biliyan 561.8 ga majalisar dokokin jihar a ranar Alhamis a Asaba.

 Ya ce kudirin gwamnatinsa na samar da ababen more rayuwa bai gushe ba.

 Gwamnan ya ce zasu mayar da hankali wajen kamalla muhimman ayyuka kamar gadar Orere ta biliyoyin naira da hanyar shiga karamar hukumar Ughelli ta Kudu, gadar Trans Warri-Ode Itsekiri da Access Road Phase 1, gadar Kwale-Beneku da gadar Ayakoromor.

 Ya ce za a kammala ayyukan ne kafin karewar wa’adin gwamnatinsa a watan Mayun 2023.

 Okowa ya ce kwangilar gadar Ayakoromor da gwamnati ta yi watsi da shi a baya-bayan nan an ba wani dan kwangilar aikin.

 “Haka kuma ana sa ran kammala aikin titin Ughelli-Asaba (Sectors A da C2) a shekara mai zuwa" a cewar Gwamnan.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci