OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Kwara: Yara Biyu Sun Tsere Bayan Masu Garkuwa Dasu Sunyi Barci

Kwara: Yara Biyu Sun Tsere Bayan Masu Garkuwa Dasu Sunyi Bar

Wasu yara guda biyu sun tsere daga hannun masu garkuwa dasu, bayan suka buƙaci a biya Naira milliyan 10 a jihar Kwara.

Yaran masu suna Jamiu da Sambo da masu garkuwa suka kama sun tsere ne daga hannun su bayan bacci ya dauki ƴan bindigar.

An yi garkuwa da su ne bayan wasu ƴan bindiga sun kashe mahaifinsu, Alfa Tunde Aribidesi a ranar Alhamis, a gidansu da ke Gaa Osibi a karamar hukumar Ilorin ta yamma a jihar Kwara.

An tafi da yaran, Jamiu mai shekaru 12,  da Sambo mai shekaru 15 yayin da masu garkuwar suka bukaci a bada Naira miliyan 10.

Sai dai yaran biyu sun tsere ne a daren Lahadi bayan wadanda suka sace su sun kwanta barci a cikin dajin.

“Masu garkuwa da mutanen sun yi amfani da wayar mahaifinmu marigayi, suka tuntuɓi ƴan uwanmu kan kudin fansa Naira miliyan 10.

"Amma mun tsere daga daji lokacin da suke barci mun isa gidanmu da sanyin safiya,” in ji Sambo.

Wani likita ya tabbatar da cewa yaran biyu suna asibiti ana duba lafiyarsu, yayin da ya tabbatar da ci gaba da basu kulawa.

Abokin marigayin, Alfa Lawal Taoheed kafun tserewan nasu yayi addu'ar Allah ya dawo da yaran lafiya yayin da ake ci gaba da tattaunawa da masu garkuwa da mutane.

Ya ce, “Iyalan sun shirya Naira miliyan 7 ta hannun wani wakili, Abin takaici, masu garkuwa da mutanen ba su gaya wa mutumin ainihin inda za su gana da su ba.

"Ko kuma inda za su ajiye kudin, wanda hakan ya sa ya dawo da su.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci