Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce gwamnati ita kadai ba za ta iya ci gaba da kula da Jami'o'i a Najeriya ba.
Shugaban kasar ya bayyana haka ne a lokacin da yake gabatar da jawabinsa kan kudirin kasafin kudin shekarar 2023 a gaban taron hadin gwiwa na majalisar dokokin kasar a ranar Juma’a.
Buhari ya ce gwamnati za ta samar da wasu matakai na samun kudaden da za a Gudanar da bangaren ilimi yadda ya kamata a Najeriya.
Shugaban ya kuma ce za a daina bayar da tallafin man fetur a shekarar 2023.
Tun tuni ministan kudi da sauran Masu ruwa da tsaki suke shawartar Gwamnatin Tarayya ta soke tallafin man fetur din da kasar take bayarwa.
A wannan karan Shugaba Buhari ya bukaci naira triliyan 19.76 a kasafin kudin shekarar 2023.
0 Tsokaci