OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

ISWAP Ta Dauki Alhakin Kai Hari Kan Jami’an ‘Yan Sandan Ondo

ISWAP Ta Dauki Alhakin Kai Hari Kan Jami’an ‘Yan Sandan

Rundunar 'yan ta'addar ISWAP ta yi ikirarin kai hari kan wata motar 'yan sanda a karamar hukumar Owo ta jihar Ondo.

Jaridar SaharaReporters ta ruwaito cewar "ISWAP ta yi ikirarin cewa mayakan ta sun kai hari kan wata motar ‘yan sanda da manyan bindigu, lamarin da ya yi sanadin lalata motar"

 Sai dai kungiyar  bata bayyana ko an samu asarar rayuka ba yayin harin. 

 Idan za'a iya tunawa a kwanakin baya kungiyar ISWAP ta kai hari a coci a Owo a watan Yuni inda ta kashe masu ibada kusan 50. Wanda tuni aka kama wadanda suka aikata wannan harin.

Da take Mayar da martani game da ikirarin kungiyar Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Oyeyemi Oyediran, ya shaidawa manema labarai a Akure cewa har yanzu ba ta samu rahoton wani hari da kungiyar ta’addancin ISWAP ta kai kan jami’anta ba.

 

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci