OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Hukumar Kashe Gobara Ta Zaƙulo Gawarwaki 2 A Kogin Ilorin

Hukumar Kashe Gobara Ta Zaƙulo Gawarwaki 2 A Kogin Ilorin

Hukumar kashe gobara dake jihar Kwara ta sanar da gano gawarwaki guda biyu biyo bayan faɗawar wata mota cikin kogin.

Motar ta faɗa ne a kogin dake unguwar Akerebiata da ke Ilorin, cewar Jaridar Daily Nigerian.

Da yake bayyana hakan, Shugaban sashen yaɗa labarai na hukumar Hassan Adekunle a wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar a Ilorin, yace a cikin kogin harda wata mota aka tsinta.  

Ya ce an tsinto gawarwakin mutanen biyu da wata mota kirar Toyota Yaris mai lamba: APP544E a kogin da ke daura da Olusola Saraki Abattoir a Ilorin.

"An samu jita-jita cewa lamarin ya faru ne a lokacin da aka yi ruwan sama a daren Juma’a a lokacin da waɗanda suka jikkata ke kokarin bi ta hanyar gadar.

“Aikin ceton ya kasance kamar aikin hadin gwiwa, Domin dukkan mutanen unguwar sun ba ƴan kwana-kwana cikakken goyon bayansu a duk lokacin aikin,” in ji Adekunle.

Don haka ya shawarci jama’a da su guji tukin mota a duk lokacin da ake yin ruwan sama mai ƙarfi.

Ya ƙara da cewa har yanzu ba a san ko su wanene wadanda abin ya shafa ba har ya zuwa lokacin gabatar da wannan rahoto.

Wannan na da nasaba da mamakon ruwan sama da aka shafe sa’o’i da dama ana tafkawa wanda yayi barna a wasu sassa na birnin llorin.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci