OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Gwamnonin Arewa 3 Na Son Marawa Obi Baya, Cewar Lauya Ajulo

Gwamnonin Arewa 3 Na Son Marawa Obi Baya, Cewar Lauya Ajulo

Wani Lauyan kundin tsarin mulki, Kayode Ajulo, ya ce gwamnoni uku daga Arewa suna so su marawa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party (LP), Peter Obi baya.

Ajulo ya bayyana hakan ne ga kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) a wata hira ranar Jumma'a. 

Ajulo yace duk da haka, Obi bai daura damaran zama shugaban kasa ba sakamokon baya samun masu ruwa da tsaki na yankunan kasan ba. 

A cewar lauyan: "Har yanzu zan ce Peter Obi bai shirya zama shugaban kasa ba saboda bai shirya tsallaka kogin Neja ba har ma da kogin Owena."

Ya kara da cewa akwai gwamnonin Arewa uku da suka nuna zasu mara wa Obi baya a zaben 2023 dake tafe. 

Yace, "Ina sane da gwamnoni uku daga Arewa da suka ba da alamun zasu goya masa baya."

Lauyan ya kuma ce yakamata Obi yayi amfani da wannan damar ya zagaya wurin duk masu ruwa da tsaki a fadin kasar nan gabanin yakin neman zaben.

Ya bukaci Obi da ya tsallake kudancin kasar nan domin zuwa yankin Arewa don neman goyon baya su. 

A cewar Lauya Ajulo, yakamata Obi ya watsar da zaman sa a kafafen yada zumunta, ya koma neman goyon baya na zahiri ta hanyar ziyartar masu ruwa da tsaki na duk fadin ƙasar nan.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci