OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Gwamnatin Zamfara Za Ta Biya Naira 10,000 Duk Wata Ga Marasa Galihu

Gwamnatin Zamfara Za Ta Biya Naira 10,000 Duk Wata Ga Marasa

Governor Bello Muhammad Matawalle

Gwamnatin jihar Zamfara ta ware naira miliyan 500 domin tallafawa marasa galihu da karfi 50,000 a jihar ta hanyar biyan su duk wata.

Kwamishinan yada labarai na jihar, Ibrahim Dosara ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi.

Kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito, Dosara ya bayyana cewa: “Za a raba Naira miliyan 500 ga masu cin gajiyar 50,000 duk wata don taimaka musu wajen tinkarar kalubalen da ake fuskanta a yanzu, da nufin bunkasa tattalin arzikin jihar. "

Sanarwar ta kara da cewa wadanda za su ci gajiyar tallafin zasu fito ne daga kananan hukumomi 14 na jihar domin biyan su Naira 10,000 duk wata.

Kwamishinan ya kara da cewa wani mataki ne da gwamnatin jihar ta dauka na rage radadin talauci a jihar.

A cewar sa: “Gwamnati ta saki karin kudaden domin raba wa masu karamin karfi da marasa galihu, duk wata a fadin kananan hukumomi 14 na jihar.

“Wannan baya ga sauran matakan tallafi na gwamnati kamar Naira 20,000 da ake raba wa mata 1,800 duk wata a fadin jihar”.

Dosara ya kara da cewa ta hanyar shirin rage radadin talauci a jihar, shirin zai rage matsalolin tsaro da jihar ke fuskanta a halin yanzu.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci