OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Gwamnatin jihar Zamfara ta rufe gidajen talabijin da na rediyo

Gwamnatin jihar Zamfara ta rufe gidajen talabijin da na redi

Photo Source: Blueprint

Gwamnatin jihar Zamfara ta bayar da umarnin rufe gidan talabijin na Najeriya (NTA) Gusau da kuma gidan rediyon tarayyar Najeriya FRCN Pride FM bisa zargin karya dokar gwamnati da aikin jarida.

 

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kwamishinan yada labarai Ibrahim Dosara ya fitar a Gusau ranar Asabar.

 

Kwamishinan ya ce sauran kungiyoyin yada labaran da aka sanya wa takunkumi sun hada da Gamji TV da Gamji FM da kuma Al umma TV wadanda ke zaman kansu.

 

Mista Dosara ya ce kwamitin tsaro na jihar ta amince da rufe tashoshin.

 

A cewarsa, an umurci kwamishinan yan sanda da ya kama tare da gurfanar da ma'aikatan da lamarin ya shafa wadanda aka kama suna karya doka.

 

A Najeriya hukumar kula da gidajen yada labarai ta Najeriya NBC ce ke kula da gidajen yada labarai wacce ake ganin tana tsauri akan gidan Radio da talabijin.

 

 

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci