OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Gwamnatin Buhari ta yi kokari wajen kawar da ta'addanci’ – Cewar Keyamo

Kakakin yakin neman zaben shugaban kasa na jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Festus Keyamo, ya ce gwamnatin tarayya ta cimma karfin Boko-Haram zuwa "kusan babu komai."

Mista Keyamo, wanda kuma shi ne karamin ministan kwadago da samar da ayyuka, shi ne ya bayyana hakan a ranar Litinin a wata hira da ya yi da gidan talabijin na Trust.

Ya kuma kare ayyukan yaba wa kokarin da gwamnatin APC ta yi a cikin shekaru bakwai da ta yi tana mulki.

Sannan Shirin ya gayyato Daniel Bwala, mai magana da yawun kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam'iyyar PDP wanda aka hada shi da ministan a zauren shirin Kasancewar Shugaba Muhammadu Buhari dan takarar jam'iyyar APC a shekarar 2015, inda jam'iyyar ta APC ta yi alkawarin tabbatar da bunkasar tattalin arziki, yaki da rashin tsaro da cin hanci da rashawa domin ciyar da kasar gaba.

Duk da munanan hare-haren da 'yan ta'adda ke kaiwa al'ummomi a wasu sassan kasar, musamman a arewacin kasar, Mista Keyamo ya ce gwamnati ta yi kokari sosai wajen rage ta'addanci idan aka kwatanta da yadda ta karbi mulki a hannun gwamnatin baya. Ya yi zargin cewa ‘yan adawa ne suka dauki nauyin duk wani labarin kanzon kurege da ake nunawa akan gazawar gwamnati APC don bata mata suna.

“Maganar cewa gwamnati ta gaza wannan wani batune da ya zama kamar waka da ‘yan adawa suka rera shi a bakin kowa ba tare da duban cikakken abin da muka yi ba, Abin da 'yan adawa suka yi a cikin 'yan shekarun shine fitar da kalmomi na bogi wanda waɗannan kalmomi suka kasance kalamai da 'yan jarida ke kai kawo a kansu wadannan kalmomi sune- gwamnati ta gaza,An kasa samar da tsaro.

“Gadon me aka bar mana? matsalar Boko Haram itace gadon da gwamnatin da ta shude ta bari A wancan lokacin 'Boko haram ta kwace kananan hukumomi sama da 14 a yankin Arewa maso Gabas tare da kafa tutocinsu. Sannan munzo mun tarar da rikicin manoma da makiyaya wanda ke faruwa tun kafin zamanin Obasanjo. Waɗannan matsaloli ne da suka dade ana fama da su.

“Ba a kawar da Boko Haram kwata-kwata ba, amma anyi kokari wajen rage ta'addancin su matuka saboda mun kulla kyakyawan alaka da mukayi da makwabtanmu Mun rage musu karfi sosai, Ba wai ina nufin cewa mun kawar da ta'addanci kwata kwata ba amma amma munci karfin rabin abinda muka tarar, ya ragu matuka sosai," in ji Mista Keyamo.

Ministan ya zargi gwamnatin PDP da ta shude kan yajin aikin da kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) ta ke yi.

Tun a watan Fabrairu ne kungiyar ta shiga yajin aikin.

Ya ce gwamnatin da ta shude ita ta fara sanya hannu kan yarjejeniyar da aka kulla tun shekarar 2009 da kungiyar sai dai gwamnatin ba ta cika alkawarin da ta dauka ba inda ta bar gwamnatin Buhari da damben zaman sasantawa da kungiyar.

“Ya za ayi ace gwamnati ta kulla yarjejeniya da ASUU kan wasu sharudda da suka san ba za su iya cikawa ba, shi ya sa ASUU ke yajin aiki. “Don haka 'yan Najeriya su sani cewa ASUU ba ta shiga yajin aiki saboda gwamnatin APC ba,ba da gwamnatin APC akayi yarjejeniya ba, PDP ce ta sanya hannu kan yarjejeniyar,” inji shi.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci