OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Gwamnan Jihar Nasarawa Ya Bada Umarnin Ɗaukar Likitoci 37 Aiki

Gwamnan Jihar Nasarawa Ya Bada Umarnin Ɗaukar Likitoci 37 A

Nasarawa state Governor, Abdullahi Sule

Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya bayar da umarnin daukar likitoci 37 aiki domin bunƙasa harkokin kiwon lafiya a fadin jihar.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ƙaddamar da wani shiri na wayar da kan jama’a a karamar hukumar Nasarawa a karshen mako, cewar Jaridar Punch.

Ya bayyana cewa daukar karin likitocin ya zama wajibi domin biyan buƙatun likitocin da za su yi aiki a cibiyoyin lafiya daban-daban a faɗin jihar.

Gwamnan, yayin da yake jaddada kudirin gwamnatinsa na samar da ingantattun ayyukan kiwon lafiya ga jama’a, ya kara da cewa, za a tura karin likitocin zuwa sabbin asibitocin da aka kammala ginawa.

Asibitocin wanda ofishin kula da ci gaba mai dorewa (SDGs) ya gina, yana mai jaddada cewa hakan zai taimaka wajen  yaɗa jinya don isa kowane yanki na jihar.

“Tun da aka fara wannan atisayen, ya zuwa yanzu ƙananan hukumomi tara ne aka gudanar da aikin ba da magani kyauta, inda aka yi wa mutane 819 tiyata, sannan bawa  marasa lafiya 18,000 da suka kamu da cututtuka daban-daban magani.  

"Waɗannan maganin sun haɗa da tiyatar ido, gwajin ganin ɗan tayi da binciken ɗakin gwaje-gwaje,” in ji Sule.

Gwamna Sule ya bayyana wasu muhimman ayyuka a fannin kiwon lafiya a karkashin gwamnatinsa da suka hada da, sayan asibitocin tafi da gidanka, da nufin saukaka magunguna da ga marasa galihu a cikin al’umma.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci