OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Gamayyar kungiyoyin farar hula na Arewa sun gargadi majalisar dinkin duniya ta guji tsoma baki a shari'ah Nnamdi Kanu.

Shugaban 'yan awaren IPOB Nnamdi Kanu

Gamayyar kungiyoyin 52 ne suke hada baki wajen Jan hankalin gwamnatin tarayya da ta lura da shishigin da ma'aikatan majalisar dinkin duniyar keyi a shari'ar Shugaban 'yan awaren IPOB Nnamdi Kanu.

Sun fitar da wannan jawabin ne Jim kaɗan bayan kammala taron kwanaki uku a birnin tarayya, Abuja.

Hakazalika gamayyar kungiyoyin ta zargi kungiyar kwadago NLC da cin amanar aluma domin ta gaza aiwatar da yajin aikin da ta alkawarta bayan karewar wa'adin data debe wa gwamnatin ta kawo karshen yajin aikin Asuu.

Hakan na Kunshe a takardar bayan taron dake dauke da sa hannun kakakin gamayyar Abdulaziz Sulaiman.

Jawabin ya ce " Muna gargadin majalisar dinkin duniya ta guji shiga alamuran Kasarnan musamman ma akan harkar Nnamdi Kanu. Hakazalika muna alawadai da cin amanar da NLC ta nuna karara nayin watsi da kudurin tafiya yajin aikin dai daya biyo bayan karewar wa'adin sati biyun data daukar wa gwamnatin tarayya ta cimma matsaya tsakanin ta da kungiyar malaman jami'o'i ta kasa ASUU"

Gamayyar kungiyoyin farar hulan ta ja hankalin yan Arewa dasu bukaci dukan dan takarar dake neman kuri'un su ya bayyana tanadin da yayi na samar da cigaban yankin su gabanni zaben 2023.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci