OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 5 Kwanaki da suka gabata

Gwamna Abiodun ya taya Amusan murnar nasarar lashe gasar tsere

Gwamna Abiodun ya taya Amusan murnar nasarar lashe gasar tse

Gwamna Dapo Abiodun na jihar Ogun ya taya gwarzuwar data lashe gasar tseren mata Tobi Amusan murnar nasarar datayi.

Amusan ta zama mace mafi sauri a tseren mita 100 na mata a wannan shekara bayan ta kammala tseren a cikin dakika 12.40s a wasan guje-guje da tsalle-tsalle da aka gudanar a Jamaica.

Amusan ta sha gaban zakaran duniya,yar asalin garin jamaica Danielle Williams wajen lashe gasar.

Gwamna Abiodun, a sakon taya murnar ya bayyana Amusan a matsayin mace mai jajircewa data zamewa jihar Ogun da Najeriya abun alfahari.

“A madadin gwamnati da na al’ummar jihar Ogun, ina matukar taya fitacciyar ‘yar mu, Tobi Amusan murnar zama mace mafi sauri a gasar tseren mita 100 na mata a shekara ta 2024, bayan ta lashe gasar a dakika12.40"

"Hakika muna alfahari da ita data bawa marar da kunya ta zama farar jakadar al'ummar kasarnan a idon duniya" in ji Gwamnan.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci