OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 5 Kwanaki da suka gabata

Za'a cigaba da shari'ar Hadi Sirika da kaninsa

Za'a cigaba da shari'ar Hadi Sirika da kaninsa

Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, ta bayyana cewa za a gurfanar da tsohon ministan sufurin jiragen sama, Hadi Sirika da dan uwansa a ranar Talata domin cigaba da gudanar da shari'a. 

 

An tuhumi mutanen biyu da tuhume-tuhume takwas a gaban babbar kotun tarayya da ke Garki a Abuja.

 

 Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta bayar da belin Sirika, diyarsa da wasu mutane biyu a kan kudi Naira miliyan 100 tare da mutane biyu da za su tsaya masa a makon jiya.

 

Ana tuhumar Sirika da sauran bisa zargin almundahanar kudi biliyan ₦2.7bn. Wadanda za a tsaya masu a cewar kotun, dole ne su mallaki kadarori a Abuja da kuma su kasance cikakkun ‘yan kasa.

 

 A cewar EFCC, laifukan da Sirika ya aikata sun sabawa sashe na 19 na dokar cin hanci da rashawa da sauran laifuka ta 2000.

 

 

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci