OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Fashewar iskar gas ta raunata mutum 5, da lalata shaguna 22, da kuma gidaje a garin Jigawa

Fashewar iskar gas ta raunata mutum 5, da lalata shaguna 22,

Hukumar tsaron farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen jihar Jigawa, a yau Talata ta bayyana cewa mutane biyar sun jikkata sakamakon fashewar iskar gas a karamar hukumar Babura ta jihar.

Kakakin hukumar NSCDC, CSC Adamu Shehu, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ga Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya a Dutse, ya kara da cewa fashewar ta kuma lalata shaguna da gidaje.

Haka kuma, jami’in hulda da jama’a na ‘yan sanda, PPRO, a jihar, DSP Lawan Shiisu, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya ce shaguna 17 da gidaje biyar sun lalace sakamakon gobarar da fashewar gas din ta haddasa.

Kakakin hukumar NSCDC, a shafin sa, ya ce lamarin ya faru ne a ranar Litinin da misalin karfe 9:00 na dare, bayan da jami’an tsaro suka yi tsaye a yankin tare da kama wata mota da ke dauke da bututun iskar gas guda 25.

Ya yi zargin cewa direban motar ya ki tsayawa wanda hakan ya sa jami’an suka bi shi, lamarin da ya sa daya daga cikin silinda ya fado daga motar inda ta kama da wuta nan take.

Kakakin ya kara da cewa motar ta taho ne daga garin Tinkim da ke karamar hukumar Magarya ta Jamhuriyar Nijar kuma ta nufi karamar hukumar Hadejia ta jihar Jigawa.

Ya ce a halin yanzu wadanda abin ya shafa suna karbar magani a babban asibitin Babura.

Hakazalika, jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Lawan Shiisu, shi ma ya tabbatar da faruwar lamarin.

Mista Shiisu ya ce, wata tawagar jami’an hukumar hana fasa kwauri ta Najeriya ta kwastam mai lamba 12 ne ke bin motar yayin da take dauke da iskar gas daga jamhuriyar Nijar.

Ya kara da cewa shaguna 17 da gidaje 5 ne suka lalace sakamakon gobarar da fashewar ta haddasa. NAN

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci