OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 2 Shekaru da suka shude

EFCC Bata Kama Kwankwaso Ba, Cewar Sanusi Dawakin Tofa

EFCC Bata Kama Kwankwaso Ba, Cewar Sanusi Dawakin Tofa

Sanata Rabiu Musa Kwankwaso| Hoto Daga: Leadership

Shugaban Kwankwaso Media Centre, Malam Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya musanta labaran dake yaduwa cewa hukumar EFCC ta kame tsohon gwannan Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

A cewar sa, Kwankwason ne ya ziyarci ofishin hukumar da kan sa don wanke sunansa kan zargin da ake yi masa.

Ya kara da cewa Kwankwaso ya ziyarci hedikwatar hukumar dake birnin tarayya Abuja, inda ya gana da wasu jami'an na EFCC na wasu awanni don wanke sunan sa.

A cikin wata sanarwa, tsohon Gwamnan yace wannan ba komai bane face siyasa.

Sanarwar ta kara da cewa, "Jita -jitar kama ni karya ce kuma mara tushe. A matsayina na dan kasa mai bin doka, ni da kaina na ziyarci hukumar a ranar Asabar don in wanke sunana kuma hakan ne abin da ya faru ke nan."

“Na hadu da su, jami’an na EFCC, na gaya musu cewa na zo ne don wanke suna na a kan takardar korafi da aka rubuta tun 2015 akai na. Na ba da amsoshin duk tambayoyin da jami’an suka yi," kamar yadda takardar ta ruwaito.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci