OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Mako da ya shude

Ministan shari'a ya bukaci Yahya Bello ya mika kansa ga EFCC domin bincike

Ministan shari'a ya bukaci Yahya Bello ya mika kansa ga EFCC

Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya (AGF) kuma Ministan Shari’a, Prince Lateef Fagbemi, SAN, ya yi kira ga tsohon Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello, da ya mutunta kanshi ya mika kansa ga jami'an tsaro domin bincike. 

A cewar wata sanarwa dauke da sa hannun ministan da aka rabawa yan jarida a ranar Alhamis, hukumar EFCC na da ikon gayyatar duk wani dan Najeriya domin yi masa tambayoyi.

Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) na neman Yahya Bello ne bisa zarginsa da aikata almundahana a lokacin da yake gwamna a jihar Kogi.

Fagbemi ya bayyana matakin da gwamnan jihar Kogi Ahmed Ododo ya dauka wanda ya yi amfani da karfin ikonsa wajen hana hukumar kama Yahya Belloa ranar Laraba a matsayin abun kunya wanda zai iya zubar da mutuncin Najeriya a idon sauran kasashen duniya.

Ministan shari'ar yace " rigimgimun da suka barke sanadiyar yunkurin EFCC su gudanar da ayyukansu bisa tsarin doka sun dawo kune na kuma wannan babbar matsalace domin dokar kasa ta bawa hukumar EFCC damar gayyatar duk wani dan kasa ya amsa tambayoyi yayin da suke gudanar da bincike saboda haka babu dalilin da zai sa wasu mutane su dinga yunkurin hana hukumar gudanar da aikin ta. Guduwa a duk sanda EFCC suka nemi mutum bazai warware matsalar ba sai ma ya dada lallata lamarin" 

"Ni na zauna bisa doran doka kuma idan na samu bayanin wata hukuma tana neman ta karya doka zan dakatar da ita amman ya kamata suma alumma su bayar da hadin kai ga dukkan hukumar data gayyace su domin basu damar gudanar da aikin su" ministan ya jaddada.

Tsarin shari'a mai inganci wanda zai iya kare duk wani mai bin doka da oda wajen neman kariya. “Don haka ina kira ga duk wanda EFCC ko wata hukuma ta gayyace shi da ya gaggauta bin tafarkin mutunci ya girmama irin wannan gayyata a maimakon daukar wani dan lokaci ko guduwa"  

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci