OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 2 Shekaru da suka shude

Da Dumi-Dumi: An Dage Sauraron Shari'ar Nnamdi Kanu

Da Dumi-Dumi: An Dage Sauraron Shari'ar Nnamdi Kanu

Latest News On Nnamdi Kanu Court Trial For Today January 18, 2022.

Wata babbar kotu dake zama a baban birnin tarayya, Abuja, ta dage sauraron shari'ar dake tsakanin gomnatin tarayya da Nnamdi Kanu.

 

An dage karar ne a yau Talata zuwa ranar Laraba.

 

Hakan ya biyo bayan korafin da Kanu yayi akan cewa gwamnatin tarayya ta gaza bashi sabbin tuhume-tuhumen ta guda goma sha biyar akan lokaci wanda kuma gomanatin ta kawo kotu.

 

Kanu, ya bayyana ta bakin lauyoyin sa, wanda Cif Mike Ozekhome yake jagoranta cewa, yana zargin gwamnati da toshe masa kofofin da za su taimaka masa wurin kare kan sa.

 

Lauyan ya shaida wa kotu cewa gwamnatin bata sanar da su akan sabbin tuhume-tuhumen ba har sai kusan sa'o'i ashirin da hudu kafin zaman kotun.

 

Haka Kuma, Ozekhome yayi watsi da tuhume-tuhumen da akayi wa Kanu.

 

A nasa bangaren masu gabatar da kara, Mohammed Labaran daga ma'aikatar shari'a ta tarayya, wanda kuma shine jagoran lauyoyin gwamnatin, yace yadda kotu ta dage shari'ar na kankanin lokaci ba abin magana bane.

 

Yace hakan zai bawa lauyoyin Kanu da shi kan sa Kanun damar nazari akan tuhume-tuhumen.

 

Haka kuma, kafin ta dage ci gaba da sauraron karar zuwa ranar Laraba, mai shari’a, Binta Nyako ta umurci hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) da ta bai wa Kanu damar canza tufafi, tare da ba shi ‘yancin yin motsa jiki.

 

Nnamdi Kanu dai shine shugaban kungiyar masu fafutukar kafa kasar Biafra (IPOB) wanda a shekarar da ta gabata aka dawo da shi Najeriya don fuskantar tuhume-tuhumen da gwamnatin kasar ke masa.

 

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci