OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Mako da ya shude

Bankuna sun yi asarar N10bn sanadiyar kutse a shekarar 2023

Bankuna sun yi asarar N10bn sanadiyar kutse a shekarar 2023

Masu ruwa da tsaki a harkar banki da tsarin hada-hadar kudi, a ranar Alhamis, sun yi tir da karuwar kutse ta yanar gizo da yayi sanadiyar bankunan Kudi (DMBs) suka yi asarar Naira biliyan 10 a rubu'i na biyu na shekarar 2023.

 

Wannan ya nuna karuwar adadin asarar kusan kashi 300 cikin 100 a duk shekara idan aka kwatanta da na shekarun baya.

 

A wani taron masu ruwa da tsaki da kamfanin Mastercard ya shirya don samar da hanyoyin magance matsalar kutse da damfara yayin hadahadar kudi mataimakiyar shugaban sashen hulda da abokan cinikayya a yankin Gabas da Yammacin Afirka a kamfanin Mastercard, Kari Tukur ta ce duk da dimbin kudade da sabbin fasahohi da aka samar da nufin yakar matsalar tsaro ta intanet, adadin kudin da aka yi hasarar a bara ya wuce kima.

 

Kari Tukur ta ce, “mun fara ganin karuwar ayyukan hada-hadar kudi na zamani a Najeriya, Amman adadin da bankunan suka you hasara ya daure min kai, duk da dimbin jarin da aka zuba a harkar kirkire-kirkire, da samar da tsaro don kare kutse ta yanar gizo, kullum matsalar dada karuwar take."

 

Ta lura cewa akwai buƙatar haɗin gwiwa tsakanin masu ruwa da tsaki "don yaƙar wannan haɓakar barazanar tsaro ta yanar gizo." 

 

Tukur ta ci gaba da cewa, kamfanin Mastercard ya himmatu sosai kan tsaron yanar gizo yayin hadahadar kudi hakan me ma yasa kamfanin ya kashe dala miliyan 250 "don taimakawa ƙananan kamafanoni su karfafa nasu tsaro ta yanar gizo."

 

Ta bayyana cewa MasterCard sun bullo da fasahohin zamani irin daban daban don maganace matsalar kutsen kamar fasahar tokenization, da biometric.

 

 

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci