OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

ASUU Ta Janye Yajin Aiki

 ASUU Ta Janye Yajin Aiki

Kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) ta yanke shawarar dakatar da yajin aikin da ta shafe watanni takwas tana yi.

 

Kungiyar ta dauki wannan matakin ne a taron majalisar zartarwa ta kasa (NEC) da kungiyar ta gudanar a Abuja a safiyar yau Juma’a.

 

Wani ɗan kungiyar ASUU-NEC da ke wajen taron ya shaida wa Premium times cewa dakatar da yajin aikin ya biyo bayan hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke a makon da ya gabata inda ta bukaci kungiyar ta bi umarnin kotu.

 

Kotun masana’antu ta bayar da umarnin ne bisa gwamnatin Najeriya ta bukaci a umurci malamai da su dakatar da yajin aikin.

 

Majiyar PREMIUM TIMES ta bayyana cewa har yanzu fa gwamnati ba ta biya bukatun malaman suka nema ba.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci