OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 2 Shekaru da suka shude

An Kashe Mutum 11 a Wani Hari Da Sojojin Ambazoniya Suka Kai Taraba

An Kashe Mutum 11 a Wani Hari Da Sojojin Ambazoniya Suka Kai

A ranar Laraba ne wasu da ake zargin sojojin Ambazoniya suka kai hari karamar hukumar Takum ta jihar Taraba.

Maharan sun shigo ne daga jamhuriyar Kamaru inda suka kashe mutum 11 har da wani basarake.

Yayin da yake tabbatar da lamarin, Joseph Manga, dan uwa ga basaraken da aka kashe ya ce maharan sun fara ne daga iyakar kasar ta Kamaru.

Ya kara da cewa sun yi kwanton bauna kafin su kashe yayan nasa daga bisani kuma suka dinga bi suna kashe wasu.

A cewar sa har yanzu ana duba cikin daji don tsinto wasu gawarwakin ko kuma kamo wadanda suka buya.

Kamar yadda rahotanni suka bayyana, ana tsammanin wasu mazauna garin da ba a gan su ba sun gudu zuwa garuruwan dake makwabtaka don tsira da rayukansu.

Shugaban karamar hukumar, Shiban Tikari ya bayyana cewa, a lokacin da ya ziyarci wurin bayan an kai musu dauki, an gano gawarwaki biyar kawai.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci