OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 2 Shekaru da suka shude

Allurar Corona: El-Rufa'i Ya Ba Maikatan Gwamnati Wa'adin Kwanaki 12

Allurar Corona: El-Rufa'i Ya Ba Maikatan Gwamnati Wa'adin Kw

Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir Ahmad El-Rufa'i| Hoto Daga: BBC

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa'i ya ba ma'aikatan gomnatin jihar wa'adin kwanaki 12 don yin allurar rigakafin Corona.

Gwamnan ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwa ranar Talata.

Sanarwan wanda mai ba gwamnan shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Muyiwa Adekeye ya fitar, yace ma'aikatan baza su shiga ofishin su ba har sai sun nuna katin shaidar rigakafin.

Dokar zata fara aiki ne a ranar talatin da daya ga watan Oktoba.

Sanarwar ta kara da cewa akwai bukatan masu ziyartar ofisoshin gwamnati da su gabatar da katin shaidar rigakafin kafin su samu shiga.

Haka kuma dole su sanya takunkumi a fiska kafin a basu damar shiga.

Sanarwar ta kara da cewa gwamnati na shawartan mazauna jihar da suyi rajista a cibiyoyin kiwon lafia don yin allurar rigakafin.

 

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci