OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

2023: Lokaci Yayi da Za’ayiwa Tinubu hallacci – Sanata Kwara

2023: Lokaci Yayi da Za’ayiwa Tinubu  hallacci – Sanata

Shugaban kwamitin majalisar dattijai kan harkokin kiwon lafiya, Dakta Ibrahim Oloriegbe, a ranar Asabar din da ta gabata ya ce kasar nan za ta yi kyau da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Asiwaju Tinubu, a matsayin shugaban kasa.​​​​​​

Sanatan Kwara ta tsakiya, wanda ya kasa samun tikitin komawa kujerar sa, ya kuma yi alkawarin yin aiki domin samun nasarar Tinubu a zabe mai zuwa.

Dan majalisar tarayya wanda ya yi magana a Ilorin yayin wata liyafar da ‘yan uwa da magoya bayansa suka shirya masa, ya kara da cewa: “Lokaci ne da ‘yan Kwara za su yiwa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC halacci”

Ya kara da cewa goyon bayansa ga Tinubu ya samo asali ne daga yadda Tinubu  mallaki halayen jagorancin kasar nan.

“Duk da abubuwan da suka faru da ni a zaben fidda gwani na jihar, na ci gaba da zama dan APC. Tun shekarar 2010 na mayar da hankalina kan abinda ya dace wanda hakanne yazama ci gaban Kwara kuma haryanzu ina  cikin wannan gwagwarmayar.”

“Na yi imanin cewa dole ne in tsaya a APC domin hada karfi da karfe wajen gyara abubuwan da ke faruwa a jam’iyyar a jihar. Mafi mahimmanci, jim kadan bayan kammala zaben fidda gwani, na samu  ganawa da Asiwaju Tinubu da abokin takararsa, Sanata Kashim Shettima. Mun yi nazarin abin da ya faru a zaben fidda gwani kuma Mun yarda duk abinda ya wuce ya wuce.

“Asiwaju Tinubu yana goyon bayan manufarmu a Kwara. A 2011, ni dan takarar Sanata ne na Action Congress of Nigeria (ACN) kuma Tinubu ne jagoranmu. A 2018/2019 ya kasance babban mai goyon bayan kungiyar ‘Otoge’ kuma ni naci gajiyar gwagwarmaya. Me yasa yanzu zan ce duk abin da ya faru da ni  saboda zaben fidda gwani , zan bar Asiwaju saboda son rai? bazai yiyuba, Goyon bayana ga Tinubu ya dogara ne akan iyawarsa da cancantarsa. Ina kuma mara masa baya don amfanin jihata domin idan Najeriya ta yi kyau Kwara za ta yi kyau. Babu  wani dalili na aikata ɓarna,” in ji Oloriegbe.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci