OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 2 Shekaru da suka shude

'Yan Bindiga Sun Kai Hari Masallaci A Taraba, Sun Kashe Mutum 1 Da Sace 7

'Yan Bindiga Sun Kai Hari Masallaci A Taraba, Sun Kashe Mutu

Wasu ‘yan bindiga sun kai hari a wani masallaci a jihar Taraba inda suka kashe daya tare da yin garkuwa da wasu bakwai.

‘Yan bindigan sun kai hari a masallacin kauyen Damrari da ke karamar hukumar Gasol a jihar Taraba a yammacin Laraba.

Harin da aka kai a lokacin buda baki ya yi sanadiyar mutuwar mutum guda.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Taraba Usman Abubakar ne ya tabbatar da harin.

Abubakar ya bayyana cewa maharan sun haura mutum 30 ne suka mamaye kauyen akan babura.

Ya kara da cewa mutumin da aka kashe ya gamu da ajali ne a lokacin da ‘yan bindigar suka yi harbe-harbe tare da yin awon gaba da wasu mutum bakwai.

Ya kara da cewa rundunar ‘yan sandan na yin duk abin da za ta iya domin ceto wadanda aka sace tare da bin diddigin wadanda suka aikata laifin.

Ya kuma bayyana cewa tuni aka tura jami’an ‘yan sandan Najeriya tare da ‘yan banga zuwa yankin da lamarin ya shafa.

Wani ganau mai suna Malam Inuwa Harbe ya shaida wa wakilin Leadership cewa ‘yan bindigan sun zo ne da kakin sojoji a yayin da suka ci karen su ba babbaka na sama da mintuna 30 a kauyen.

Harbe ya bayyana cewa mazauna yankin sun kai rahoton sirri ga jami'an tsaro akan haduwar ‘yan bindiga a dajin da ke kusa da garin amma ba a yi komai ba.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci