OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Yan Bindiga Sun Kai Hari Kauyuka 8 A Kebbi

Yan Bindiga Sun Kai Hari Kauyuka 8 A Kebbi

Daruruwan jama'a ne daga kauyuka takwas a karamar hukumar Augie dake jihar Kebbi suka yi gudun hijara biyo bayan harin da ƴan bindiga suka kai ƙauyukan na su.

Ƙauyukan sun hada da; Zafi, Tungur Rafi, Tungar Tudu,Keke, Kwaido, Sabon garin Kwaido, Tungar chichira da kuma Tattazai.

Mazauna kauyen sun bar kauyukan su bayan da Yan bindigar suka Kai yankin Zagi a ranar labarar da ta gabata, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na ƙasa ya ruwaito.

Harin yayi sanadiyar mutuwar mutane uku yayin da mutane da dama suka samu raunuka. Yan bindigar sun kuma yi nasarar yin gaba da mutane 15 daga cikin su.

Dagacin garin Zagi, Malam Muhammadu lawali-Sule ya bayyanawa jaridar Vanguard cewar maharan sun yi dirar mikiya a kauyen ne da misalin sha biyu na dare. 

Yace sunyi iya bakin kokarin su kare kansu daga maharan amma abin yaci tura har suka ci galaba a kansu.

Malam Muhammadu lawali-Sule ya kuma bayyana cewar tuni suka mika wadanda suka jikkata zuwa asibiti domin karbar agaji.

Kwamishinan Yan Sandan jihar, Ahmed Magaji kantagora yace sun tura karin ma'aikata zuwa yankin domin tsaurara tsaro.

Ya kuma tabbatar da cewar rundunar Yan Sandan tayi wa Yan bindigar kawanya domin hana su guduwa da wadanda sukayi nasarar sacewa da zummar yin garkuwa da su.

Ya kuma ce suna sa ran kamasu nan bada dad'e wa ba.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci