OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Yajin Aiki: Ɗalibi Mai Karatun Likitanci Ya Zama Ɗan Kasuwa A Sokoto

Yajin Aiki: Ɗalibi Mai Karatun Likitanci Ya Zama Ɗan Kasuw

Sakamakon  yajin aikin da kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) take yi ya mayar da Usman Abubakar-Rimi, ɗalibi mai karatun likitanci da tiyata a jami’ar Usmanu Danfodiyo Sokoto (UDUS)  ɗan kasuwa.

Da yake zantawa da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a ranar Juma’a a Sokoto, Abubakar-Rimi ya ce ya zama mai sayar da abinci don rayuwa mai inganci bayan yajin aikin da malaman jami’o’in gwamnati sukeyi.

Mai sayar da abincin, wanda ya ke alfahari da sana'ar tashi ya mallaki wani katafaren kantin sayar da kayan abinci a yankin Diflomasiyya a cikin birnin Sakkwato, ya ce yajin aikin da ASUU take yi ya ba shi damar fara sana’ar.

“Na dauki hayar shago, inda na dauki ma’aikata takwas masu sarrafa shayi da abinci na Indomie, ina sayar da kayan sha na kwalba da gwangwani, shinkafa da wake, miya da nama.

“Ana sayar da farantin abinci daga Naira 200 zuwa sama dangane da bukatun abokin ciniki.”

Abubakar-Rimi ya kuma mallaki wani shago a titin Fodio shima a cikin birnin Sokoto inda yake sayar da kayan mata, hula, jakunkunan dalibai, da takalma.

“A koyaushe ina farin cikin ganin cewa na zama ma’aikacin ƙwadago saboda a halin yanzu na ɗauki mutane 10 aiki a cikin shagunan biyu.

"Na dogara ga shagunan saboda ba na tambayar iyayena kudi duk da cewa an rufe makarantu," in ji shi.

Game da yadda ya samu jari a kasuwancinsa, ya ce: “Na yi amfani da damar COVID-19 na kulle-kulle, a lokacin na fara kasuwancin rarraba kwai da kaji inda na yi hulɗa da gidajen abinci.

“Nakan kuma samu ƙwai da kajin daga manyan gonaki daga ƙananan kuɗi zuwa masu yawa, daga kuɗin da na fara kasuwancin biyu.

“Lokacin da na zamo Likita, zan shiga aikin da ba zai dauki lokaci mai yawa ba saboda a halin yanzu, na fara cire sha'awar aikin samun albashi.

 “Ina so in kafa kantin magani, in yi aiki a wani asibiti mai zaman kansa sannan in tsunduma cikin wasu kamfanoni masu zaman kansu da suka dace da sana’ata,” Abubakar-Rimi ya bayyana.

A ƙarshe Ya roki shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya lalubo bakin zaren yajin aikin, inda ya yi kira ga malaman suma su yi la’akari da radadin da dalibai suke ciki, su sasanta da gwamnatin tarayya.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci