OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 2 Shekaru da suka shude

Yadda 'Yan Sanda Suka Kama Dan Ta'adda, Wanda Ya Kashe Mutum 20

Yadda 'Yan Sanda Suka Kama Dan Ta'adda, Wanda Ya Kashe Mutum

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta kama wani mai suna Naziru Sani, wanda ake zargin dan ta’adda ne a karkashin kasurgumin shugaban ‘yan ta’adda, Bello Turji.

Naziru mai shekaru 25 ya amsa laifin kashe mutane 20 a jihohin Zamfara da Sokoto da Katsina da ke Arewa maso Yammacin Najeriya.

Da aka kama shi, ya ce daga sama da mutane 200 na sansanin Turji, yana hada kai wajen kai hare-hare wa al’ummomin yankin.

Da aka tambaye shi ko nawa ake biyan sa, ya bayyana cewa duk kudin fansa da aka basu (’yan kungiyar), ana biyan kowannen su tsakanin N20,000 zuwa N30,000.

Wanda ake zargin ya ce shi dan kauyen Makera ne da ke karamar hukumar Tsafe a jihar Zamfara.

Ya kuma bayyana cewa Bello Turji yana zaune ne a dajin Jangebe na jihar Zamfara inda yake bada umarni.

Da yake amsa tambayar yadda aka kama shi, ya ce, “Ina kan hanya ta zuwa Suleja (Jihar Neja) ne ‘yan sanda suka kama ni da sassafe a karamar hukumar Funtua ta jihar nan (Katsina). Na bar matata da ‘ya’ya na a Zamfara”.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Katsina, Gambo Isah ne ya tabbatar da faruwar lamarin.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci