OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Wani Yaro Dan Shekara 18 Ya Shake Mahaifiyar Sa Har Lahira

Wani Yaro Dan Shekara 18 Ya Shake Mahaifiyar Sa Har Lahira

Wata Kotun Majistare da ke Akure a ta bayar da umarnin tsare Tope Momoh mai shekaru 18, bisa zarginsa da shake mahaifiyarsa mai shekaru 52, Stella Momoh har lahira.

 

 Dan sanda mai shigar da kara, Nelson Akintimehin, ya ce an gurfanar da wanda ake tuhumar ne da laifin kisan kai.

 

 A cewar Akintimehin, wanda ake zargin ya aikata laifin ne da tsakar daren ranar 6 ga watan Satumba, 2022, a Ikakumi Akoko, cikin jihar Ondo.

 

 Ya shaida wa kotu cewa Tope ya shake mahaifiyarsa har lahira a tsakiyar dare saboda ta kira shi da shege.

 

 Ya ce wanda ake tuhumar ya amsa cewa shi ya kashe mahaifiyarsa makonni biyu bayan an binne ta.

 

 Mai gabatar da kara ya ce ba a san musabbabin mutuwar Stellah ba a lokacin da ta mutu har sai da danta ya amsa cewa shi ne ya aikata laifin.

 

 Akintimehin ya kara da cewar "Tope, yayi ikirarin nadama ce ta sanya ya shaida wa 'yan uwansa cewa ya shake mahaifiyarsa har lahira a lokacin da ta tashe shi da tsakar dare,tana yi masa ruwan tsinuwa tare da kiran sa da shege."

 A nasa bangaren wanda ake tuhumar ya roki kotun cewa: “Ban samu natsuwa ba tun lokacin da aka binne mahaifiyata. Shi yasa na fadi gaskiyar cewa ni na shake ta har ta mutu. Don haka ina rokon kotu ta tausaya min.”

 

 Sai dai mai gabatar da kara, ya bukaci kotun da ta ci gaba da tsare wanda ake kara a gidan yari, har zuwa lokacin da za a Yankee hukunci.

 

 Babban alkalin kotun Musa Al-Yunnus ya bayar da umarnin a tsare wanda ake zargin a gidan gyaran hali na Olokuta.

 

Hakazalika, Musa Al-yunnus ya dage ci gaba da sauraren karar har zuwa ranar 20 ga watan Oktoba domin yanke hukunci.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci