OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Wani ya kashe kanin sa dan shekara 12 yayin gwajin maganin bindiga

Wani ya kashe kanin sa dan shekara 12  yayin gwajin maganin

Nigerian Police force

Rundunar ‘yan sandan jihar Kwara ta tabbatar da mutuwar wani yaro dan shekara goma sha biyu da dan uwan sa ya harbe yayin da yake gwada ingancin wata maganin bindiga. 

Lamarin dai ya faru ne a garin Kaiama dake jihar Kwara.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa ‘ya’yan sun ‘karfafa’ kansu da kayan tsafi lokacin da suka yanke shawarar gwada ingancin sa.

Kakakin rundunar ‘yan sandan, SP Ajayi Okasanmi ne ya bayyana hakan a ranar Litinin a Ilorin, babban birnin jihar.

Okasanmi ya ce wan yaron ya dauki bindigar tokan mahaifin su ya harbe dan uwan sa domin gwada ingancin maganin. 

Ya kara da cewa yaron ya mutu nan take bayan harbin sa.

A cewar sa: “Su biyun ‘ya’yan wani Abubakar Abubakar, mafarauci a garin Dutse Gogo da ke karamar hukumar Kaiama a jihar Kwara.

“Mai laifin ya tsere cikin daji nan da nan bayan aikata laifin.

“An fara bincike kan lamarin.

"An shawarci iyaye da masu kula da su da su sanya ido kan ayyukan 'ya'yan su tare da guje wa yin wasu abubuwa a gaban su don hana afkuwar hakan."

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci