OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Tambuwal zai mai da daliban Sokoto 55 da yakin Ukraine ya koro su Jami'ar Baze

Tambuwal zai mai da daliban Sokoto 55 da yakin Ukraine ya ko

Aminu Tambuwal

Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal na shirin mayar da dalibai 55 na jihar da suka dawo daga kasar Ukraine jami'ar Baze dake Abuja.

Daliban da ke karatun likitanci da sauran kwasa-kwasai masu alaka da su, an tilasta musu barin karatun su ne suka dawo Najeriya sakamakon mamayar da Rasha ke yi a Ukraine.

Babban sakatare a hukumar ba da tallafin karatu na jihar Sokoto Bello Isa ne ya bayyana wa manema labarai hakan.

Isa ya ce gwamnati za ta kashe Naira miliyan 500 a duk shekara domin karatun su wanda hakan kashi 50 cikin 100 ne na abin da gwamnati ke kashewa a lokacin da suke kasar waje.

A cewar sa: “Yanzu jihar za ta rika kashe Naira miliyan 500 a duk shekara wajen gudanar da karatun su, wanda kashi 50 ne na abin da muke kashewa a kan su lokacin da suke kasar Ukraine.

“Lokacin da suke kasar Ukraine, muna kashe sama da Naira biliyan daya wajen biyan kudaden karatun su da alawus alawus din su.

“Kuma kun san abubuwa ba kaman da ba.

“Jihohin kasar da dama na kokawa kan biyan albashin ma’aikatan su.

"Don haka ne a ganawar da muka yi da iyaye da shugabannin daliban, mun gaya wa kan mu gaskiya mai daci."

Ya kuma kara da cewa, dukkan bangarorin sun amince da shigar da daliban Jami’ar Baze tare da jaddada cewa jami’ar tana da kayan aiki masu inganci.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci