OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Sojojin Najeriya: Wata Kungiyar Matsa Mai Zaman Kanta ta yabawa Sojojin kan Fatattakar Yan Ya Ta'adda

Sojojin Najeriya: Wata Kungiyar Matsa Mai Zaman Kanta ta yab

Wata kungiya mai rajin kawo ci gaban matasa, Northern Youth Network, ta yabawa sojojin Najeriya bisa nasarorin da suka samu a yunƙurin kawo ƙarshen ayyukan kungiyoyin yan ta'adda na ISWAP, BokoHaram, ƴan fashi da wasu muggan laifuka a ƙasar nan a wata guda da ya wuce.

A wata ganawa da manema labarai, Malam Abdulrahman Ahmed, shugaban kungiyar ya mika sakon yabo ga sojojin Najeriya a wani tara da suka gabata a babban birnin tarayya Abuja.

 Ahmed ya ci gaba da cewa sama da makwanni hudu ke nan, biyo bayan umarnin shugaban kasa Muhammadu Buhari ga sojojin Najeriya kan kara kaimi wajen yaki da makiya kasa. 

Kuma daga wannan lokacin zuwa yanzu, sojoji tare da temakon bayanan sirri daga sauran kawayen su na hukumomin tsaro irin su, DSS, DIA, NIA, sun yi nasara wajen gudanar da ayyukan su.

Abdulrahman ya ci gaba da cewa tunda ISWAP/BokoHaram da ‘yan bindiga suka yi amfani da yakin gorilla, ana bukatar tattara bayanan sirri sosai kafin a samu nasara a yakin, kuma zuwa yanzu hakan ya fara tabbata lura da yadda jami'an saka sami nasarorin ruguje sansanonin ‘yan bindiga da dama a dazuzzukan tafkin Chadi, Kaduna, Zamfara Neja, Yobe da Borno sun fada hannun sojojin Najeriya.

Daga bisani, mallam Abdulrahman Ahmed ya yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya ci gaba da baiwa sojojin Najeriya goyon baya musamman bangaren tattara bayanan sirri domin tsaro na zamani ya ta’allaka ne kan tattara bayanan sirri da kuma tsayawa tsayin daka na kawar da duk wani abu da ke barazana ga tsaro a kasar. (Blueprint )

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci