OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Harin Ta'addanci: DSS Ta Bukaci Al'umma Su Kwantar Da Hankula

Harin Ta'addanci: DSS Ta Bukaci Al'umma Su Kwantar Da Hankul

Hukumar Tsaro ta DSS ta bukaci ‘yan Najeriya da su kwantar da hankalinsu, amma kuma su yi taka-tsan-tsan, biyo bayan sanarwar da ofishin jakadancin Amurka da ke Abuja ya fitar cewa za a iya kai harin ta’addanci a cikin wannan mako.

 Hukumar ta DSS a cikin wata sanarwa da kakakinta Dr. Peter Afunanya ya fitar ta shawarci ‘yan Najeriya da su yi taka-tsan-tsan, hukumar ta tabbatar da cewa za ta hada kai da sauran hukumomin tsaro domin wanzar da zaman lafiya.

Afunanya ya ce a cikin sanarwar da aka fitar da misalin karfe 11:20 na dare ranar Lahadi. “DSS ta samu tambayoyi da dama dangane da shawarwarin tsaro da ofishin jakadancin Amurka da ke Abuja ya bayar. Akwai bukatar Jama'a su tuna cewa ofis ɗin ya ba da irin wannan gargaɗi daban-daban a baya"

Sanarwar ta kara da cewa "Yayin da yake ba da shawarar cewa kowa da kowa ya ɗauki matakan da suka dace, an umurci jama'a da su taimakawa hukumomin tsaro da bayanai masu amfani game da barazanar harin Yan ta'adda."

  "A halin da ake ciki, Hukumar ta yi kira da a kwantar da hankula yayin da take aiki tare da sauran jami'an tsaro da masu ruwa da tsaki don wanzar da zaman lafiya a ciki da wajen Abuja," 

A halin da ake ciki Mazauna Abuja tuni Suka shiga zulumi game da sanarwar ofishin jakadancin Amurka.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci