OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Rundunar Yan Sanda Ta Kama Wata Farfesa Data Doki Yar Sanda

Rundunar Yan Sanda Ta Kama Wata Farfesa Data Doki Yar Sanda

Nigerian Police force

Rundunar ‘yan sandan ta cafke wata lauya mai zaman kanta a Abuja, kuma mai fafutukar kare hakkin bil’adama, Farfesa Zainab Duke Abiola, bisa zargin cin zarafin ‘yar sandar da take gadin ta Insifekta Teju Moses.

 

 Farfesan, wanda aka kama ta tare da yar aikinta, Rebecca Enechido, an ruwaito cewa, ta ci zarafin Yar sandar ne saboda kin yin wasu ayyukan cikin gida da ta sanya ta.

 

 Zainab Duke, ‘yar fafutuka haifaffiyar Mbaise, ta ci zarafin Yar sandar tare da hadin gwiwar Yan aikinta a ranar Talata, 20 ga Satumba,a gidanta da ke Garki, Abuja, saboda ta ki bin dokar ta nayin aikin cikin gida.

 

A cikin wani faifan bidiyo da ya bazu a ranar Laraba, an ga jami’ar kwance cikin jini,tana neman a kai ta asibiti domin kula da lafiyarta.

 

Jami’in hulda da jama’a na rundunar, CSP Muyiwa Adejobi, wanda ya tabbatar da kamen a wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis, ya ce rundunar ‘yan sandan ta baza komar ta domin kama wani ma’aikacin gida da ya gudu wanda ya hada baki da farfesan wajen kai harin.

 

 Ya ce babban sufeton ‘yan sanda, Usman Alkali Baba, ya yi Allah-wadai da kakkausar murya tare da bayar da umarnin a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kuliya.

 

 Ya ce, “Sufeto Janar din ya yi Allah-wadai da mummunan harin da aka kai wa wata jami’ar ‘yan sanda, Insifekta Teju Moses, da shugabarta, wadda lauya ce kuma mai fafutukar kare hakkin bil’adama, Farfesa Zainab Duke Abiola da ma’aikatan gidanta da suka hada da yar aikin gidan, wata Rebecca Enechido suka yi da wani namiji da ake zargi a halin yanzu"

 

 Adejobi ya ce, IGP din ya bayar da umarnin janye dukkan jami’an ‘yan sandan da ke da alaka da Farfesan, ya kuma nuna rashin jin dadinsa kan yadda wani mutum da ke ikirarin kare hakkin bil’adama zai iya keta hakkin wani.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci