OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 2 Shekaru da suka shude

Rundunar Sojin Saman Najeriya Ta Ceci Mutane 26 A Kaduna

Rundunar Sojin Saman Najeriya Ta Ceci Mutane 26 A Kaduna

Hoto Daga: Guardian

Rundunar sojin saman Najeriya ta musamman ta ceto mutane 26 da aka yi garkuwa da su a jihar Kaduna.

An ceto wadanda lamarin ya rutsa da su ne a hanyar Birnin Gwari zuwa Kaduna ranar Laraba.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun mai magana da yawun Rundunar, Air Commodore Edward Gabkwet.

Gabkwet ya bayyana cewa, jami’an tsaron na musamman ne suka kai dauki domin ceto wadanda lamarin ya rutsa da su bayan sun gano motoci guda biyar da ke nuni da cewa an kwashe mutanen da karfi.

Sojojin sun gudanar da bincike mai nisan kilomita 3 a cikin daji kafin su ceto wadanda lamarin ya rutsa da su.

Wadanda lamarin ya rutsa da su sun bayyana cewa ‘yan bindigan sun rabu kashi uku kana suka kewaye su.

‘Yan bindigar sun gudu tare da wasu mutane bayan sun ga sojojin yayin da sauran wadanda abin ya shafa suka boye a cikin daji.

Sanarwar ta kuma kara da cewa an kai wadanda harin ya rutsa da su zuwa asibitin NAF 461 dake Kaduna domin duba lafiyarsu.

A halin yanzu dai ana ci gaba da aikin ceto sauran wadanda aka sacen tare da bin sawun 'yan bindigan.

 

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci