OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Mako da ya shude

An gurfanar da mutumin daya sace miliyan 1.2 daga asusun bankin mamaci a gaban kotu

An gurfanar da mutumin daya sace miliyan 1.2 daga asusun ban

 ‘Yan sanda a ranar Alhamis sun gabatar da wani matashi mai shekaru 30, John Timothy, a gaban wata kotun majistare da ke Iyaganku, Ibadan bisa zargin satar Naira miliyan 1.2 daga asusun ajiyar wani mamaci. 

Wanda ake karar, yana fuskantar tuhuma kan laifukan hada baki da yin sata sai dai ya musanta aikata laifin. 

Dan sanda mai gabatar da kara, Insfekta Olalekan Adegbite, ya shaida wa kotun cewa wanda ake tuhuma ya aikata laifukan ne tsakanin ranar 17 ga watan Mayun 2021 zuwa ranar 21 ga watan Yulin 2021.

Adegbite ya yi zargin cewa wanda ake kara ya saci Naira miliyan 1.2 daga asusun wani marigayi Mista Johnson David dake bankin Access.

 Ya kuma shaida wa kotun cewa wani dan marigayin mai suna Mista Daniel David ne ya gano satar.

Ya ce laifukan sun ci karo da sashe na 516 da 390(9) na dokokin laifuka na jihar Oyo na shekarar 2000. 

Alkalin kotun, Oluwabusayo Osho, ya bayar da belin wanda ake kara a kan kudi naira 500,000 tare da masu tsaya masa guda biyu. Ya kuma dage sauraron karar zuwa ranar 7 ga watan Mayu.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci