OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Bankin Fidelity Ya Samu Ribar Naira Biliyan 241

Bankin Fidelity Ya Samu Ribar Naira Biliyan 241

Bankin Fidelity ta samu riban Naira biliyan 241.8 a cikin kwata na uku na shekarar 2022.

Wannan ya nuna kashi 38.73 idan aka kwatanta da Naira biliyan 174.354 da suka samu a daidai wannan lokacin na shekarar 2021.

Bankin ya samu ƙaruwar kashi 46.32% na Riba da kuɗin ruwa daga rance da ci gaba, wanda ya ƙaru daga Naira biliyan 111.5 a shekarar 2021 zuwa Naira biliyan 163.209 a shekarar 2022.

Kuɗin shiga daga kuɗin ruwa da lamuni yana da gudummawar kashi 82%.

A tsawon lokacin da ake magana, kuɗaɗen shiga sun ƙaru zuwa Naira biliyan 25.042 daga Naira biliyan 21.762 a shekarar 2021.

Kuɗaɗen da ake samu daga ATM sun ƙaru da kashi 70.48% zuwa Naira biliyan 6.521 daga Naira biliyan 3.825 a Q3 2021.

Yayin da riba bayan haraji ya ƙaru zuwa Naira biliyan 34.959 a kwata na uku na shekarar 2022, ƙaruwar kashi 31.86% idan aka kwatanta da Naira biliyan 26.512 a shekarar 2021.

A cewar bankin, ƙaruwar kuɗaɗen shiga ya samo asali ne sakamakon karuwar lamuni da kuma samun yanayin ƙaruwar kuɗin ruwa.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci