OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Likitan Kwara Ya Kashe Budurwarsa Ya Binne Gawa A Ofis

Likitan Kwara Ya Kashe Budurwarsa Ya Binne Gawa A Ofis

Nigerian Police force

Rundunar ‘yan sandan jihar Kwara ta ce jami’anta sun cafke wani likita mai suna Adio Adeyemi, na babban asibitin Kaiama bisa zargin yin garkuwa da wasu mata biyu.

 

Ana zargin Adeyemi da yin garkuwa da kuma kashe budurwar sa mai suna Ifeoluwa, da wata matar aure mai suna Nofisat Halidu a shekarar 2021.

 

An bayyana bacewar Ifeoluwa a yankin Tanke, yayin da Nofisat, wata matar aure a Kaiama, mijinta Mista Halidu ya kai cigiyarta wajen Yan Sanda.

 

 Rundunar ‘yan sandan ta tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan, SP Ajayi Okasanmi, ya fitar ranar Lahadi.

 

 Sanarwar ta kara da cewa, " yayin da ake bibiyar wasu korafe-korafe da wasu ‘yan kasa suka rubuta, CP, Paul Odama ya fara bibiyar batun wata mace da ta bace, Nofisat Halidu a karamar Hukumar Kaiama ta Jihar Kwara, ranar 21 ga Nuwamba, 2021.

 

 A bisa umarnin CP, an fara gudanar da bincike kan lamarin tun a ranar 30 ga Satumba, 2022. Mun samu tallafin rundunar Yan Sandan jihar Edo da suka kama Wani Aduo Adeyemi Adevowale wanda ya amsa laifin kashe budurwarshi me suna Ifeoluwa, ya kuma jefar da gawarta a dajin unguwar Alapa a Ilorin a shekarar 2021.

 

La'akari da cewar shine Shugaban Babban Asibitin Kaiama a wancan lokacin rundunar Yan Sandan jihar Kwara ya jagoranci tawagar zuwa babban asibitin Kaiama, inda aka tilasta bude ofishin wanda ake zargin.

 

Ganin an Malala sabon siminti a ofishin ya sanya shakku a zukatan ma'aikatan, hakan yasa aka fasa wajen aka buma zakulo gawar Wata mace da ba'a san ko wacece ba.

 

 Bayan bincike ne aka gano cewar gawar Nofisat Halidu ce wadda mijinta ya bade' Yana cigiyar ta.

 

 “Sauran abubuwan da aka gano a ofishin likitan da aka tsare sun hada da wayoyin hannu guda biyu da Jakunkuna na mata guda biyu, gashin mata, mayafi da wando na Miata.

 

 Sanarwar ta kuma bayyana cewar Kwamishinan Yan Sandan jihar Kwara ya Nemi hadin kan  rundunar ‘yan sandan jihar Edo da suke tsare da likitan inda ta bukaci a sako wanda ake zargin ga rundunar ‘yan sandan jihar Kwara domin amsa wasu tambayoyi dangane da sakamakon binciken da aka gano a ofishinsa.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci