OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Kwara: 'Yan Sanda Sun Tabbatar Da Sace Jami'i Da 'Yan Bindiga Suka Yi

Kwara: 'Yan Sanda Sun Tabbatar Da Sace Jami'i Da 'Yan Bindig

Nigerian Police force

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kwara, Paul Odama ya tabbatar da sace wani dan sanda mai suna ASP Abdulmumini Yusuf a jihar da wasu ‘yan bindiga suka yi.

Kwamishinan ya ce tuni rundunar ‘yan sandan jihar ta fara gudanar da bincike a yayin da take aikin ceto tare da kamo da kuma gurfanar da wadanda suka aikata laifin.

A cewar sa: "Eh, gaskiya ne, amma har yanzu muna kan aikin."

Jami’in da ke aiki a ofishin shiyya na ‘yan sanda a Ilorin an yi garkuwa da shi ne a daren ranar Talata a lokacin da yake shirin shiga gidan sa.

Wata majiya a yankin ta bayyana wa jaridar Punch a yau cewa kwamishinan ‘yan sandan ya ziyarci yankin.

A cewar majiyar: "Mun lura da cewa an yi ta sintiri da jami'an 'yan sanda a kewayen anguwan sakamakon kasancewar kwamishinan 'yan sandan."

Haka kuma, sakataren kwamitin ba da shawara kan harkokin tsaron na al'umma a jihar, Shola Muse ya koka kan karuwar kalubalen tsaro a cikin jihar yayin da ya yi kira da a kara himma daga hukumomin tsaro domin shawo kan lamarin.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci