OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 2 Shekaru da suka shude

Kotu Ta Kori Shugabannin APC A Jihar Taraba Saboda Saba Ka’idojin Zabe

Kotu Ta Kori Shugabannin APC A Jihar Taraba Saboda Saba Ka�

An kori shugabannin jam'iyyar APC na jihar Taraba sakamakon hukuncin da wata kotu ta yanke a jihar.

Alkalin babbar kotun tarayya da ke zama a Jalingo, jihar Taraba, Mai shari’a Simon Amobeda ya ce zaben jam’iyyar da aka gudanar a ranar 24 ga watan Oktoban 2021 ya saba ka'ida.

‘Yan jam’iyyar da suka fusata sun shigar da kara a gaban kotu inda suka ce an gudanar da zaben ne ba bisa ka’idojin kundin tsarin mulkin jam’iyyar ba.

Alkalin ya ce zaben ya saba wa umarnin kotu da ya hana jam’iyyar gudanar da zaben.

Lauyan wanda ake tuhuma, Barr. John Odekena ya ce bayan tuntubar wanda yake karewa, za su daukaka kara kan hukuncin a kotun daukaka kara.

Yayin da take bayyana gamsuwa da hukuncin, lauya ga mai kara, Barr. Joy Ezekiel ta ce wadanda ake tuhumar sun kasa baiwa sauran ‘yan jam’iyyar sanarwar sa’o’i 24 kafin su gudanar da zaben.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci